Accessibility links

Masanan kimiyya a kasar Amurka suna kira ga wani magani mai inganci da zai iya kai ga warkar da cutar kanjamau.

Masanan kimiyya a kasar Amurka suna kira ga wani magani mai inganci da zai iya kai ga warkar da cutar kanjamau.

A wani bincike da aka yada ranar Alhamis a wata jaridar magani ta New England, likitocin jami’ar Pennsylvania suka fitar da dan kwan naman jiki na jini daga masu cutar kanjamau 12 kuma sukayi amfani da wata fasaha suka fitar da kwayar protain wadda ta bar kwayar cutar ta shiga cikin kwayoyin jini. Likitocin sunyi allurar kwayoyin jinin baya ga marasa lafiyar, daganan suka dena basu maganin su na cutar zuwa wata daya.

Kwayar cutar ta dawo ga dukan marasa lafiyar sai dai guda daya kawai, amma likitocin sun gano cewa kwayoyin jinin da akayiwa magani sun nuna alamar warkewa daga kwayar cutar. Sakamakon wannan binciken ya nuna cewa wasu marasa lafiyar zasu dena shan maganinsu na kullum na tsaida kamuwa.

Bayan haka kuma, likitoci a wani taron cutar kanjamau a Boston ranar laraba sun baiyyana cewa wani jariri na biyu a Amurka wanda aka haifa da cutar kanjamau yanzu bashi da alamun kwayar cutar, godiya domin cin nasarar shan magani sosai da sauri bayan haihuwar ta asibitin sashin Los Angeles shekarar da ta wuce.

Ruhoton fari na wannan ya faru ne a (Kudancin jihar Mississippi), a inda wata yarinya data kamu da cutar aka sata a maganin cutar kimanin sa’a 30 bayan an haife ta. Likitoci sun cigaba da ba yarinyar magani har sai da ta kai wata 18, sannan uwar ta dena kaita ga maganin.

Lokacin da uwar ta maida yayinyar ga magani bayan watanni da yawa, likitoci sun gano babu wata alamar cutar kanjamau a cikin jinin ta. Yarinyar yanzu shekarunta uku kuma bata da cutar.

Wata kungiyar masu kimiyya ta California suna kokarin aiwatar da wani bincike wanda gwamnatin Amurka ta biya, wanda zai duba idan yin magani na wurwuri ga jarirai da suka kamu da cutar kanjamau zai kyale su dena amfani da maganin idan gwaji ya nuna cewa basu da kwayar cutar a tsawon lokaci.
XS
SM
MD
LG