Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masanin Girke-Girke Anthony Bourdain Ya Rasu


Anthony Bourdain

Anthony Bourdain kwararre a fannin girke-girke da ake watsa shirye-shiryensa a gidan talbijin na CNN, ya rasu. Bayanai sun ce Bourdain ya kashe kansa ne.

Fitaccen masanin girke-girke, wanda ya shahara wajen yin tsokaci kan dandanon abinci a duniya, Anthony Bourdain ya rasu, yana mai shekaru 61.

Abokin Bourdain, Eric Ripert ne ya tsinci gawarsa a dakin otel dinsa da safiyar jiya Juma’a a Faransa, inda suka je aiki kan wani shiri da za a watsa a kafar talbijin ta CNN, a shirin da ake wa lakabi da “Parts Unknown” a turance.

A cewar gidan talbijin din na CNN, Bourdain ya kashe kansa ne.

An haifi Bourdain a New York, ya kuma yi kuruciyarsa ne a Leonia, wata unguwa da ke wajen birnin New Jersey.

Ya kammala karatunsa na jami’a a makarantar koyon girke-girke ta Amurka a shekarar 1978.

Daga nan ne kuma ya samu damar yin aikace-aikace a gidajen sayar da abinci a New York, inda ya samu daukaka daga mukamin mai wanke-wanke har zuwa shugaban girke-girke.

Kafin ya fara aiki da CNN a shekarar 2013, Anthony ya jagoranci wani shirinsa na kansa da yake tafiye-tafiye mai suna “No Reservations.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG