Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Coronavirus Sun Kai 81 a Najeriya - NCDC


Dakin gwajin cututtuka da magunguna
Dakin gwajin cututtuka da magunguna

Hukumar kare yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta ce adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus ya kai 81.

Adadin ya karu ne bayan da aka samu wasu mutum 16 da aka tabbatar sun harbu da cutar.

“A ranar 27 ga watan Maris 2020, an samu karin mutum 16 dauke da cutar COVID-19 a Najeriya.” In ji shafin yanar gizon hukumar ta NCDC.

“Ya zuwa yanzu, jimullar mutum 81 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya, an sallami mutum uku sannan mutum daya ya rasu sanadiyyar cutar ta COVID-19.” Hukumar ta kara da cewa.

Daga cikin sabbin mutum 16 da aka gano dauke da cutar a ranar 27 ga watan Maris, 8 a Legas suke, 3 a Abuja, 2 a Oyo, 2 a Enugu sannan 1 a Edo, a cewar NCDC.

Sai dai hukumar ta ce, dukkan sabbin mutanen da aka gano suna da cutar ba sa cikin mummunan yanayi kuma suna samun kulawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG