Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Dakon Kaya Sun Tafi Yajin Aiki A Lagos


Matuka manyan motocin dakon kaya suka cika kan manyan hanyoyin faransa domin nuna rashin amincewarsu da shirin garambawul din fansho.
Matuka manyan motocin dakon kaya suka cika kan manyan hanyoyin faransa domin nuna rashin amincewarsu da shirin garambawul din fansho.

Masu manyan motoci wanda ke dakon kaya sun fara yajin aiki a birnin lagos domin adawa da dokara hana zirga zirga a titunan birnin daga karfe 6 na safiya zuwa 9 na dare.

Hakan ya biyo bayan umarnin da gwamnatin jihar Lagos ta yiwa masu motocin dakon kaya a birnin cewa su kiyaye hanyoyin birnin karfe 6 na safiya zuwa karfe 9 na dare. Uwar kungiyar masu motocin dakon kayan sun fara wani yajin aiki yajin aikin da sai baba ta gani, domin tilastawa gwamnatin jihar janye wannan umarni nata.

Yanzu haka dai harkokin yau da kullum na neman tsayawa cik a babbar tashar jiragen ruwa na kasar inda akasarin masu dakon kayan ke dauko kayansu zuwa wasu sassa daban daban na Najeriya. wannan lamari ya shafi masu hada hadar harkar gwari a birnin na Lagos, al’amarin da ka iya tada farashin kayayyakin saye da sayarwa dama na kasuwanni daban daban dake jihar dama wasu sassa na tarayyar Najeriya.

Mataimakin shugaban masu dakon kaya a jihar lagos Alhaji Abdullahi Jiji, yace “aikin mu ma da rana ya aka kare ballan tana ace daga karfe tara na dare zuwa karfe shida na safe, sau dayawa ana kwace musu motoci da kaya ballantana da daddare. Kuma ba zamu iya aiki a wannan lokacin ba.”

Suma masu amfana da dagon da motocin keyi sun yi kira ga gwamnatin jihar Lagos ne da ta duba wannan doka da nufin sassauta shi

Wakilin Muryar Amurka Babangida Jibril, ya halarci taron satantawa da yan kungiyar da kuma kwamishinan yansanda inda aka tashi taron ba tare da matsayi ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG