Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Gabatar da Kara A Italiya Suna Neman Gaggauta Shari'ar PM Berlusconi


Hoton budurwa 'yar kasar Morocco da ake kira da inkiyar Ruby,wacce ake zargin PM Berlusconi ya biyata kudi domin ya yi lalata da ita.

A Italiya masu gabatar da kara sun bada labarin zasu gabatar da bukata gaban kotu cikin mako gobe na neman a sanya shariyar PM Silvio Berlusconi, kasar cikin sahun wadanda za’a gaggauta sauraro.

A Italiya masu gabatar da kara sun bada labarin zasu gabatar da bukata gaban kotu cikin mako gobe na neman a sanya shariyar PM Silvio Berlusconi, kasar cikin sahun wadanda za’a gaggauta sauraro.

Ana zargin PM da biyan wata ‘yar karamar yarinya karuwa domin lalata,da kuma amfani da ikonsa ta yadda bai kamata ba.

Bayan sun gabatar da wan nan bukatar ce wani alkali a birnin Milan zai dauki kwanaki biyar ya duba ko akwai isashen shaidar gurfanadda Mr.Berlusconi.

Masu gabatar da kara suna zargin PM dan shekaru 74 da haifuwa da lalata da wata yarinya ‘yar kasar Morocco mai shekaru 17 da haifuwa wacce take aiki a wani Club lokacinda ta ziyarci gidansa.

Dukkansu biyu sun musanta zargin,kodashike yarinyar wacce sunanta ta yanka Karima El-Mahroug an biyata dala dubu tara domin ta halarci liyafar da aka shirya a gidan PM.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG