Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Minista Silvio Berlusconi Na Italiya Zai Gurfana Gaban Kotu


Silvio Berlusconi, firayim ministan Italiya

Ana zargin firayim ministan mai shekaru 74 da haihuwa da laifin biyan wata yarinya 'yar shekara 17 kudi domin yin lalata da ita a gidansa

Wani alkali na kasar Italiya ya umurci firayim minista Silvio Berlusconi da ya gurfana gaban kotu bisa zargin cewa ya biya wata yarinya ‘yar shekaru 17 da haihuwa yayi lalata da ita, ya kuma yi amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba.

Yau talata alkalin ya bayar da wannan umurni a birnin Milan, yana mai cewa za a fara gudanar da wannan shari’a a ranar 6 ga watan Afrilu.

Masu gabatar da kararraki sun ce Mr. Berlusconi ya biya yarinyar ‘yar kasar Morocco kudi yayi lalata da ita a gidansa. Firayim ministan mai shekaru 74 da haihuwa ya musanta wannan zargin, yayin da ita ma yarinyar ta musanta cewa ta yi lalata da shi.

Har ila yau ana zargin Mr. Berlusconi da laifin yin amfani da mukaminsa domin ganin ‘yan sanda sun saki wannan yarinyar a bayan da suka tsare ta bisa zargin sata.

Karuwanci dai ba laifi ba ne a kasar Italiya, amma biyan yarinyar da shekarunta bai kai 18 ba domin yin lalata da ita haramun ne karkashin dokokin kasar.

XS
SM
MD
LG