Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Kutse Na Shirin Satan Bayanai a Najeriya


Sanarwar da hukumar bunkasa bayyanan kimiyar sadarwa ta fitar kan barazanar kai wa Najeriya hari ta yanar gizo ya sa majalisar dattawan kasar tsayar da kudurori biyu domin kare kasar daga duk wata barazanar sace bayyanai ta yanar gizo ko yada labaran karya.

An an karar da Najeriya akan hari ta yanar gizo da za'a iya kai wa naurori masu kwakwalwa cikin kasar, musamman ma akan bankuna da wasu ma'aikatun gwamnati.

Hukumar bunkasa bayanan kimiyar sadarwa ce ta fitar da sanarwa da ta bayyana kalubalen a fili.

Hukumar ta ce masu satar bayanai na shirin kawo farmaki kan kafofin sadarwan Najeriya.

A cewar hukumar hakan ya zama wajibi kafofin gwamnati da kamfanoni da masu zaman kansu su samar da garkuwa daga wannan barazanar.

Yin hakan ya hada da kaucewa yanar gizo ta kyauta idan ba ya zama dole ba.

Kaucewa musayar hotuna ko aikawa da sako tsakanin wayoyin salula ta manhajar Bluetooth barkatai da sanya garkuwar yaki da abubuwa da kan illarta na'urori masu kwakwalwa ta hanyar yanar gizo.

An karawar ta kai zauren Majalisar Dattawan Najeriya inda aka zanta akan lamarin.

Wannan lamari ya sa, Majalisar Dattawa ta gudanar da muhawara kan wannan barazana.

Saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya domin jin wannan muhawara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG