Sassan Najeriya sun yi fama da rikici iri daban-daban da suka hada da na kabilanci, addini, siyasa,manoma da makiyaya, da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da fashi da makami da dai sauran su.
Wasu daga cikin mutanen da wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka, Zainab Babaji ta zanta da su akan wannan batu sun ce shugabannin al’umma da na addini suna da rawar da ya kamata su taka.
Haka kuma kaucewa daukar doka a hannun jama'a maimakon sasantawa zai taimaka kwarai da gaske wajen samar da zaman lafiya da fahimta a cikin al’umma.
Alhaji Abubakar Sadeeq yace duk lokacin da rikici ko rashin fahimtar juna ya kunno kai, to kamata yayi a baiwa zuciya magana sannan a kai batun gaban magabata sai a samu fahimtar juna.
Ga Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum