Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Motocin Dakon Kaya a Nijer Sun ce a Dakatar da Sabon Haraji


Motocin Dakon Kaya
Motocin Dakon Kaya

Hadakar kungiyar masu motocin dakon kaya a jamhuriyar Nijer sun yi barazanar shiga yajin aiki muddin aka ci gaba da sabon shirin haraji akan su.

Shugaban hadakar kungiyoyin Alhaji Adamu, yace idan haka ta faru hakan zai shafi illahirin ‘yan kasar da tattalin arzikin Nijar baki daya.

Kungiyar ta bayyana matukar damuwa ainun game da yadda mambobinta suke kokawa a kan rashin aiki sakamakon yadda wasu takwarorin su daga kasashe makwabta suke kasha musu kasuwa a cikin gida da waje.

Shuwagabannin Kungiyar masu motocin sun ce wannan al’amari na yin barazana ga harkoki masu motocin. Shugabannin sun fada cewar motocin su na iya share watanni da dama basu samun aiki a kasashe kamar Togo, Ghana, Benin Cote d’Ivoire da sauransu.

Kungiyar masu motocin ta yi kira ga majalisar dokokin kasar jamhuriyar Nijer tayi watsi da sabon tsarin harajin da ake shirin soma azawa motocin dakon kaya a shekara mai zuwa bisa la’akari da yanda harkokin nasu ke huskantar barazanar durkushewa.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG