Accessibility links

Masu neman buraguzon jirgin samn fasinjan Asiya sun gano wasu manyan abubuwa guda biyu a cikin teku

  • Jummai Ali

Wani yake nuna taswirar yankin da ake zaton jirgin saman fasinjan Asiya ya bace

Masu aikin neman buraguzon jirgin saman fasinjan Asiya samfurin jet sunce sun gano ko kuma sun hango wasu manyan abubuwan guda biyu a karkashin teku da nisan mita talatin.

Masu aikin neman buraguzon jirgin saman fasinjan Asiya samfurin jet sunce sun gano ko kuma sun hango wasu manyan abubuwan guda biyu a karkashin teku da nisan mita talatin.
Jami'in dake kula da aikin neman ya fadawa yan jarida a yau Asabar cewa, suna kokarin gane ainihin abubuwan da suka hangon.
Jami'an kasar Indonesia sunce ya zuwa yanzu an zakulo gawarwarkin mutane talatin bayan da a jiya Juma'a aka gano gawarwarkin mutane da dama, yawancinsu jirgin mayakan ruwan Amirka ne ya gano su.
Jirgin saman fasinjan samfuin Airbus, yana dauke da fasinjoji dari da sittin da biyu da ma'aikatan jirgin a lokacinda ya bace daga na'urar nazari ko kuma na'aurar lura da zirga zirgan jiragen sama a ranar Lahadin data shige.
Masu nazarin yanayi sunyi hasashen cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake ci gaba da tapkawa hade da iska mai karfi, zai ci gaba da jawo cikas ga yunkurin neman jirgin da gawarwarki har zuwa gobe Lahadi.

XS
SM
MD
LG