Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zaman Makoki Sun Yi Wa Gawar John Lewis Ban Kwanan Karshe


John Lewis casket public viewing
John Lewis casket public viewing

A yau talata an sake ajiye gawar marigayi dan majalisar dokokin Amurka kuma dan gwagwarmayar ‘yancin dan adam John Lewis, a ginin majalisar dokoki na Capitol a Washington DC.

An ajiye gawar ne domin masu zaman makoki su yi masa ban kwana na karshe.

Lewis ya mutu a makon jiya yana da shekara 80 bayan ya kwashe shekara daya yana fama da cutar kansa wato daji.

A jiya litinin ne aka rako akwatin gawartasa da ke lullube da tutar kasar zuwa harabar majalisar, inda ya kwashe shekaru 33 yana wakiltar jama’arsa na gundumar Goergia.

Yadda mutane suka yi ta zuwa yi masa ban kawana
Yadda mutane suka yi ta zuwa yi masa ban kawana

Kafin isowa harabar majalisar Capitol Hill, sai da jerin gwanon motocin da ke dauke da gawar, ya bi ta muhimman wurare da ke da alamun fafutukar kare hakkin dan adam, ciki har da sabon wuri nan da ke kusa da fadar White House dake nuna “Black lives Matter” wato Rayuwar Bakar fata na da muhimmanci.”

A jawabin ta jiya a harabar Majalisar, shugabar majalisar wakilai Nancy Pelosi, ta bayana Lewis a matsayin babban mai hangen nesa na majalisar.

Tace, ya bi sahun jajirtattu irin su tsohon shugaban Amurka Abraham Lincoln a wajen da aka ajiyeshi. Wuri ne na zinare da ake ajiya akwatun gawa yayin irin wannan ban kwana.

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG