Accessibility links

Masu zanga-zanga sun farma Shugaban wuccin gadin Mali

  • Ibrahim Garba

Dagarawan tsaron kasa kenan ke sa ido yayin da ake zanga-zanga Mali

Masu zanga-zangar da su ka kutsa cikin harabar Fadar Shugaban Kasar Mali

Masu zanga-zangar da su ka kutsa cikin harabar Fadar Shugaban Kasar Mali, su ka kai hari kan shugaban wuccin gadin kasar, wanda sai da aka ruga da shi asibiti a Bamako, babban birnin kasar.

Ma’aikatan asibitin sun ce an salami Shugaban wuccin gadin Mali din, Dioncounda Traore, bayan an masa jinyar gaggawa.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar ya gaya wa wakilin Muryar Amurka a Bamako (Anne Look) cewa ran Mr. Traore sam bai cikin hadari. To amman ba a san tsananin rauninsan ba.

An cimma Mr. Traore aka masa duka a yau Litini, kwana guda bayan da Kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS da kuma sojojin da su ka yi juyin mulki a Mali su ka amince cewa zai cigaba da rike mukamin shugaban kasar wuccin gadi har bayan ranar Talata, lokacin da wa’adinsa zai cika.

Masu zanga-zanga sun kutsa harabar Fadar Shugaban Kasar a yau Litini sun a bukatar Mr. Traore ya yi murabus. Shugaban ma’aikatansa, Souleymane Niafo, ya gaya wa Muryar Amurka cewa ‘yan kutsen sun ci karfin dogarawan tsaro suka danna cikin Fadar, inda su ka farma Mr. Traore a ofishinsa.

XS
SM
MD
LG