Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga Zanga Sun Yi Tattaki a Yini Na Biyu a Amurka


Masu zanga zanga yayin da suke tattaki a birnin St. Louis da ke jihar Missouri
Masu zanga zanga yayin da suke tattaki a birnin St. Louis da ke jihar Missouri

A yini na biyu a jere, masu zanga zanga sun yi tattaki a birnin St Louis da ke jihar Missouri da ke Amurka a jiya Asabar, bayan da wata kotu ta wanke wani dan sanda farar fata da aka tuhuma da kisan wani bakar fata.

Daruruwan mutane sun yi tattaki zuwa wasu sassan birnin St. Louis da ke jihar Missouri, inda aka ji suna kirarin nan na “Black Lives Matter” wato “rayukan bakaken fata ma na da muhimmanci” da sauran kiraye-kiraye, yayin da suke tattakin.

Zanga zangar ta faro ne daga ranar Juma’a, bayan da kotun ta wanke dan sanda mai suna Jason Stockley, wanda yanzu ba ya aiki da rundunar ‘yan sanda ta St. Louis, daga laifin kisan Anthony Lamar Smith, bayan da suka yi gujeguje a mota a watan Disambar shekarar 2011.

Masu shigar da kara sun zargi Stockley, da laifin dasa bindiga a kusa da gawar Smith domin ya nuna cewa yana dauke da makami.

Akalla mutane 23 ‘yan sanda suka ce sun kama yayin wannan zanga zanga, sannan ‘yan sanda tara sun ji rauni yayin wata ‘yar arangama da suka yi da masu boren.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG