Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-Zangar Adawa A Najeriya Sun Fantsama Kan Titunan Manyan Biranen Kasar

Zanga-zangar adawa da cin zarafin da ‘yan sanda ke yiwa jama’a a Najeriya ta ci gaba da gudana a kasar har tsawon mako guda yayin da masu zanga-zangar suka yi ta mamaye titunan manyan biranen kasar, suna hana zirga-zirga tare da tsayar da harkokin kasuwanci.

Masu zanga-zangar adawa da cin zarafin da ‘yan sanda ke yiwa jama’a a Najeriya sun bazama kan tituna a fadin kasar da ta fi yawan jama’a a Afirka.

An ci gaba da gudanar da zanga-zanga a birni mafi girma a Najeriya, Lagos, da kuma a kudu maso gabashin biranen Fatakwal da Uyo.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG