Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Da Biden Na Ci Gaba Da Yakin Neman Zabe


Shugaban Amurka Donald Trump na jam’iyyar Republican da abokin adawarsa na jam’iyyar Democrat Joe Bidden sun koma yakin neman zabe ranar Juma’a 16 ga watan Oktoba bayan da kowannensu ya yi taron amsa tambayoyin masu kada kuri’a a wurare daban-daban wanda aka nuna ta talabijin.

Trump da Biden sun kai ziyara jihohi 3 da ke da tasiri sosai yayin da zaben na ranar 3 ga watan Nuwamba ke karatowa a kokarinsu na neman goyon bayan masu kada kuri’a, da ya zuwa yanzu mutum miliyan 18 suka riga suka kada kuri’unsu, a cewar wani shiri na sa ido kan zabukan Amurka a jami’ar Florida.

Trump ya je Florida da Georgia, jihohin da ke kudancin kasar da ake gani suna da muhimmanci ga Shugaban wajen samun nasarar lashe zaben karo na biyu.

Shugaban ya yi jawabi a Ft. Myers da ke jihar Florida game da kare masu yawan shekaru kafin daga bisani ya halarci wani gangamin yakin neman zabe da aka yi a Ocala a jihar ta Florida da kuma Macon a Georgia.

Shi kuma Biden ya je Southfield da ke Michigan inda ya yi jawabi akan fadada damar samun inshorar lafiya mai sauki kafin ya halarci wani taro da aka yi a Detroit a jihar Michigan inda ya yi kira ga jama’a da su kada kuri’unsu kafin ranar zabe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG