Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata BIyar Sun Kai Hare Haren Kunar Bakin Wake A Chadi


Hukumomi a kasar Chadi sun ce a kalla wadansu mata ‘yan kunar bakin wake biyar suka kai hare hare a wadansu wurare biyu kusa da kan iyakar Najeriya suka kashe a kalla mutane 33 da suka hada da ‘yan asalin kasar Chadi da kuma ‘yan Najeriya dake gudun hijira a kasar.

Nan take ‘yan sanda suka dora alhakin harin da aka kai a garin Baga Sola kan kungiyar Boko haram mai tsats-tsauran ra’ayin addinin Islama.

‘Yan sanda da jami’an asibiti sun ce a kalla mutane hamsin kuma suka ji raunuka sakamakon hare haren da aka kai a garin dake takfin Chadi.

Janar Banyaman Cossingar yace an dana daya bom din ne a kasuwar kifi, yayinda aka dana sauran biyu a sansanan ‘yan gudun hijira dake bayan garin.

Makon da ya gabata, hukumomi suka ce mayakan kungiyar Boko Haram sun yi arangama da sojojin kasar Chadi kusa da tafkin Chadi. Wata majiyar soji tace an kashe sojoji goma sha daya da mayaka sha bakwai a musayar wutar.

Kasar Chadi tana daya daga cikin manyan kasashen dake bada gudummuwa a rundunar hadin guiwa da aka kafa ta yakar kungiyar Boko Haram wadda ta fara kai hare hare kasashen dake makwabtaka da Najeriya da suka hada da Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar, banda Najeriya inda kungiyar ta sami asali

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG