Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata da Yara Na Fuskantar Matsalar Rayuwa a Borno


Dubban mata da yara a sansanonin 'yan gudun hijira

Wasu kungiyoyin mata a jihar Borno sun bayyana mata da yara a matsayin wadanda ke fama da matsalar cin rayuwa da talauci.

Irin rigingimun da suka addabi arewa maso gabashin Najeriya musamman jihar Borno wadda ta kasance mahaifar Boko Haram su suka jefa mata da yara kanana cikin halin lahau-walakawati.

A wani taron manema labarai da wasu kungiyoyin mata suka kira a garin Maiduguri sabili da tunawa da ranar mata ta Majalisar Dinkin Duniya wadda ta ware ranar 8 ga watan Maris na kowacce shekara. Matan basu iya sun gudanar da bikin ba a lokacin saboda shirye-shiryen zaben shugaban kasa.

Wata shugabar kungiyar da ake kira Women for Peace and Security ta bayyana irin halin da mata suka shiga a jihar Borno da shiyar arewa maso gabas. Tace idan akwai kashe-kashe mata da yara ne suke shan wahala. Tayi misali da sansanonin 'yan gudun hijira inda yawancin mtanen dake ciki mata da yara ne. 'Yan ta'ada sun kashe iyaye maza. Mata ne suka shiga wahala domin dole su nemi yadda zasu ciyar da 'ya'yansu.

Ta cigaba da kiran duk wadanda suke da hali su taimakawa mata da yaran da suka tagayyara saboda tashe-tashen hankali. Banda taimaka masu da abinci da sutura ya kamata a basu jari su yi sana'a domin su samu madogara.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG