Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Dake Takaba Sun Ce Aikin Yi Za A Ba Su


Dan sandan Najeriya yana gadi a Marte, Jihar Borno
Dan sandan Najeriya yana gadi a Marte, Jihar Borno

Matan da aka kashe mazajensu a Jihar Nassarawa sun ce su na bukatar aikin yi domin kula da 'ya'yansu, a bayan da gwamnonin Arewa suka ba su agajin Naira miliyan 100

Matan da aka karkashe musu mazaje a rikicin garin Alakiyo dake Jihar Nassarawa, sun yi rokon da a samar musu da ayyukan yi domin su samu hanyar kula da 'ya'yansu da suka zamo marayu.

Matan sun yi wannan rokon ne a yayin da shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, Babangida Aliyu, yake mika gudumawar Naira miliyan 100 ga masu takabar a madadin jihohin arewa, kuma a yayin da gwamnan Jihar Ebonyi shi ma yake mika gudumawar buhu dubu daya na shinkafa ga matan.

Matan sun ce samun hanyar da zasu rika aiki su na ciyar da 'ya'yansu da kula da su, ita ce zata tabbatar da dorewar rayuwarsu na dogon lokaci, maimakon gudumawar da idan ya kare ba su da wata hanyar.

Gwamnan Jihar ta nassarawa, inda wannan abu ya faru, Tanko Almakura, yayi alkawarin za a nazarci dukkan bukatun matan dake takaba da iyalansu kafin a yanke shawarar yadda za a raba musu wannan gudumawa. Haka kuma yace gwamnatinsa zata yi bakin kokarinta na ganin an kula da iyalan mamatan.

Wakiliyarmu Zainab Babaji, ta aiko da cikakken bayani daga Lafia, babban birnin Jihar Nassarawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG