Accessibility links

An Yi Hasarar Rayuka A Jihar Nassarawa

  • Grace Alheri Abdu

Hanyar zuwa Lafia daga cikin garin Akwanga, Jihar Nassarawa, a bayan rikicin da ya faru a Alakyo. Matan 'yan sandan da aka kashe sun tare hanyar, su na jimamin mazajensu da aka kashe, abinda ya haddasa cunkoson ababen hawa.

An kashe 'yan sanda da dama a lokacin da suka yi yunkurin kamo madugun wata bkungiyar asiri da ake kira Ombatse

Wani rikici da ya barke a garin Alakyo dake karamar hukumar Lafiya a jihar Nassarawa ya yi sanadin rasa rayukan mutane da dama, akasarinsu 'yan sanda.

Wannan al'amari ya faru a lokacin da 'ya'yan kungiyar asiri ta Ombatse, ta 'yan kabilar Eggon, suka yi kwanton bauna suka far ma 'yan sandan da suka je neman kama madugun wannan kungiya, bisa zargin cewa yana tara makamai tare da haddasa fada a yankin.

Tuni gwamnan jihar, Tanko Almakura,ta sanar da fadar shugaban kasa dangane da lamarin wanda tun farko ya haramta kungiyar sabili da cin zarafi da tursasawa al’umma da ake zarginta da yi.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG