Accessibility links

Mata Sun Fusata Saboda Rashin Daukan Matakin da Ya Dace Akan Tsaron


Rashin Tsaro Ke Kawo Hijira

Kungiyoyin Mata Na Arewacin Najeriya Sun Fusata Dangane da Rashin Daukan Matakin da Ya Dace

Kungiyoyin mata na arewacin Najeriya, sun kalubalanci majalisar dattawa a matsayinsu na wakilai mutane masu hurumin sa ido da tsawatarwa ga bangaren zartarwa.

Matan sunce matsalolin da kasar ta ke ciki a yanzu yaba iya kawo koma baya ga damokradiyar da kasar ke morewa a yanzu.

Sun kara da cewa al'umar kasa basu samu wal-wala kamar yanda ya kamata saboda halin rashin tsaro a yankin na arewacin kasar.

Hajiya Maryam Dada Ibrahim,daya daga cikin shuwagabani kungiyoyin, tace jama'a ne suka zabi 'yan majalisu sabo da haka wajibi ne akan su dasu nemi hanyoyin magance duk wani abunda ya taso masammar wanda ya shafi tsaro.

Matan sun kara da cewa kwamitocin da aka kafa chan baya yakamata a binciko rahoton su a aiwatar da abinda ya kamata.
XS
SM
MD
LG