Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Sun Kafa Gidauniyar Tallafawa 'Yan Gudun Hijira daga Diffa, Nijar


Sakatariyar gidauniyar ke mika kayan taimakowa wata 'yar gudun hijira daka Diffa

Biyo bayan rikicin Boko Haram wanda ya daidaita wasu a yankin Diffa mata masu kamfanonin dake zaman kansu sun kafa wata gidauniya a cibiyar yada al'adu dake ofishin jakadancin Amurka domin tallafawa mutanen Diffa.

A cibiyar al'adu ta ofishin jakadancin Amurka a Nijar aka gudanar da gidauniyar a karkashin shugabancin jakadiyar Amurka dake kasar wato Jakadiya Redeck.

Mata da suka mallaki kamfanonin kansu suka kafa gidauniyar da zummartaimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita a yankin Diffa cikin Nijar din.

Maryama Dauda babbar sakatariyar kungiyar tace sutura babban abun ne shi ya sa suka maida hankali akan tara sutura domin su raba. Tace duk wanda bashi da sutura bashi da mutunci. Dalili ke nan da suka kira bangarori daban daban da kungiyoyi su tattara tufafi. Ko riga daya mutum ya kawo zata yiwa wani anfani a yankin Diffa.

Ministan al'umma Madam Kafaratu Jaku ta kira al'ummar Nijar su kawo kowane irin kayan sawa ne, tsoffi da sabbi duka suna bukata.Suna bukatan kayan yara ma.

Ministar al'umma ta Nijar Madam Kafaratu Jaku a dauniyar tallafawa 'yan gudun hijira tana mika taimako
Ministar al'umma ta Nijar Madam Kafaratu Jaku a dauniyar tallafawa 'yan gudun hijira tana mika taimako

'Yan gudun hijira a yankin Diffa na cikin wani hali na tsaka mai wuya, inji Madam Jibo Halima Hassan wadda ita ma 'yar yankin Diffa ce. Tace mata sun haihu a hanya lokacin da suke gudu. Mutane sun taka wajen kilomita saba'in ba takalma a kafafuwansu

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

XS
SM
MD
LG