Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwar Kungiyar 'Yan Tawaye Ta Kunno Kai A Nijar


Tsohon madugun 'yan tawayen Nijar Kaocen Maiga

Wani sako da aka bayyana ta faifan bidiyo ya nuna wani Adum Cikin Kodinga dauke da makami tare da wasu askarawansa su ukku suna ikirarin kafa sabuwar kungiyar tawaye saboda su yaki abun da suka kira mayar dasu saniyar ware a alamuran kasarsu ta Nijar

Mutumin Adum Cikin Kodinga ya kira kansa shugaban rikon kwarya ne na kungiyar kuma yayi jawabi ne da harshen tubawa na kabilar Tuba wanda kuma aka fasara zuwa harshen faransanci.

Kungiyar mai suna MJMN tace sakamakon rashin ganawa da hukumomin Nijar ne ya sa suka dauki makamai su nuna fushinsu akan yadda aka waresu cikin dangi ana tauye masu hakki na 'yn kasar Nijar, laifin da suka dora akan gwamnati da kamfanin kasar Nijar mai hako man fetur a rijiyoyin Agadem dake yankin Diffa.

Sai dai tuni 'yan kasar ta Nijar suka fara tofa albarkacin bakinsu akan wannan sabon labarin bullar wata kungiyar 'yan tawaye.

Kakakin tsohon kungiyar 'yan tawaye Kaocen Maiga dake rike da mukamin darakta a cibiyar bincike domin samar da zaman lafiya a yankunan Sahel da Sahara yayi tsokaci akan labarin.

Yace sun yi bincike akan tawaye kuma a ganinsa wannan sabuwar kungiyar 'yan tawaye ta tubawa bata tabbata ba domin akwai abubuwa da yawa da za'a lura dasu kafin a ce kungiyar tawaye ta tabbata.

Maiga yace yakamata a ce suna da mayaka. Na biyu a ce suna da kayan aiki. Na ukku yakamata a ce suna da wuri inda za'a iya nemansu. Na hudu yakamata a ce suna da bukatu da suka zana da suke son a biya masu. Abu na karshe shi ne suna da abubuwan da suka zana zasu yi idan ba'a biya bukatunsu ba.

A nashi ra'ayi Alhaji Salisu Ahmadu wani dan rajin kare hakkin dimokradiya na ganin daukan makami domin bayyana fushi a matsayin wani tsohon yayi. Demokradiya ta ba kowa 'yanci ya fito yayi fafutika ko kuma a yi maci kan tituna. Ya kirasu da babbar murya su fito su zauna kan teburin shawara a warware matsalarsu.

Kakakin gwamnatin Nijar Asmana Malam Isa ya ki yace komi saboda wai har yanzu gwamnatin tana kallon labarin a matsayin jita-jita amma idan suka samu bayani a hukumance zasu sanarda kowa matakin gwamnati.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG