Accessibility links

Matan sun rarraba kayan abinci, sutura da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum ga 'yan'uwansu matan da suka rasa mazajensu a rikicin Boko Haram

Mata 'yan asalin Jihar Borno dake zaune a Abuja, babban birnin Najeriya, sun kai dauki ga 'yan'uwansu mata na jihar da suka rasa mazajensu a tashin hankalin Boko Haram.

Wadannan kayayyakin agajin da suka aika ta hannun uwargidan gwamnan jihar, Hajiya Nana Kashim Shettima, sun hada da shinkafa, sukari, sabulu, har da ma tsabar kudi Naira dubu 5 ga kowace daga cikin wadanda aka taimakawa.

Hajiya Yabawo Kolo, babbar darekta a ma'aikatar harkokin mata ta jihar Borno, wadda ta wakilci uwargidan gwamnan wajen rarraba kayan, ta ce kimanin mata 200 daga kowace karamar hukumar jihar zasu samu wannan agajin.

Uwargidan shugaban majalisar karamar hukumar birnin Maiduguri, Hajiya Inna Abdulqadir Rahe, ta bayyana rokon Allah Ya ba matan da suka rasa mazajen nasu hakuri da juriyar kula da 'ya;yan da aka barsu da su.

Wasu daga cikin matan da suka samu wannan agajin sun bayyana godiya sosai da wannan agajin da suka ce zasu ci moriyarsa sosai ganin irin ukubar da suka shiga. Sun yaba ma matan da suka kawo musu wannan tallafin.

Kusan dukkan wadannan matan dai mazajensu ne ke samar musu da abin ci na yau da kullum da sauran kayayyakin bukatu. An kashe mazajensu an bar su da 'ya'ya da yawa, wasu ma an kona musu gidaje da dukkan abubuwan da suka mallaka.
XS
SM
MD
LG