Accessibility links

Wasu ‘yan bindiga a yankin gabashin Ukraine, sun kwace ayyukan gudanarwar ofishin ‘yan sanda,a daidai lokacin da ake ci gaba da hayaniya da zanga-zanga nuna goyon bayan amincewa hadewa da Rasha.

Ministan Ma’aikatar ayyukan tsaron gida ta Ukraine Arsen Avakov, ya bayyanawa cewa ‘yan bindigar sun je ne suka killace illahirin ciki da wajen har da zagayen ginin ofishin ‘yan sandan dake Slovyasnsk dake da tazarar kilomita 60 daga birnin Donetsk da safiyar yau Asabar inda suka komai ya tsaya cik.

A halin da ake ciki, magoya bayan akidojin Rasha dake zanga-zanaga na ci gaba da mamaye ofisoshin Gwamnati a Slovyansk da Luhansk.

Kuma mukaddashin friminista yayi alkawarin cimma wasu daga cikin bukatun masu zanga-zangar, bayan da wa’adin da aka bayar na janyewar masu zanga-zangar daga dukkan gine-ginen da suke mamaye dasu.
XS
SM
MD
LG