Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakan 'Yan Takarar Shugabancin Amurka Zasu Yi Ta Su Muhawarar


A yau Talata da marece ne ‘yan takaran mataimakan shugaban kasa a zaben shekarar nan ta 2016 a nan Amurka, Tim Kaine na Democrats da Mike Pence na jam’iyyar Republicans zasu gwabza a muhawarar da zasuyi da juna a garin Farmville dake jihar Virginia.

Wannan muhawarar tana zuwa ne kamar mako daya bayan muhawarar farko da aka buga a tsakanin iyayen-gidansu masu takaran shugaban kasar – Hilary Clinton (D) da kuma Donald Trump ®, muhawarar da ta kara karfafa gwiwar ‘yan Democrats, ta sa jikin ‘yan Republicans kuma yayi sanyi, bayan da ra’ayoyin jama’a daga baya suka nuna cewa Hillary din ce ake ganin tayi galaba a muhawarar, yayin da Trump ya kasa, sannan kuma yazo ya rinka abkawa cikin wasu al’amurra na cece-kucce dake dada janyo mishi samaki – kamar musayar magangannun da ya rinka yi da wata mace mai suna Alicia Machado da ta tsaya gasar Sarauniyar Kyau ta duniya, wacce kuma ya rinka zolaya akan cewa ta cika kiba.

XS
SM
MD
LG