Accessibility links

Mataimakin Ministan Kudi Ngama ya Mayarwa Gwamna Geidam Martani


Gwamnan Yobe Ibrahim Geidam
Wanda ya taba zama mataimakin gwamna Ibrahim Geidam a fannin harkoki da jama'a da yanzu ya canza sheka zuwa jam'iyyar PDP kuma yana aiki da karamin ministan kudi Yarima Ngama ya soma sukar tsohon ubangidansa.

Sule Ado Kwaki Yusuf da aka fi sani da lakani Castro wanda da ya kira gwamnan Yobe Ibrahim Geidam Bura-bura ya ce ya ji labari gwamnan na kiran sabon maigidansa wato Yarima Ngama yaro wanda bashi da kowa a jihar Yobe kuma wai ba dan siyasa ba ne. Bisa ga wadannan kalamun na gwamnan Yoben ya sa shi Sule ya kira taron manema labarai domin ya mayarda martani a madadin sabon ubangidansa.

Sule ya ce idan gwamna Ibrahim Geidam zai ce Yarima Ngama bashi da kowa a Yobe to ai kalwa ce take gayawa manda baki. Ai Ibrahim Geidam din ne bashi da kowa a Yobe domin mutum ne da bai taimaki jama'arsa ba.Duk alkawura da ya yiwa mutane ya karya. Amma Dr Yarima Ngama babu wani alkawari a kansa. Ibrahim Geidam ne ya yi masu alkawari suka bishi duk cikin kananan hukumomi suna fafitikar neman masa kuri'u suna ta yiwa mutane alkawura amma kawo yanzu babu alkawari daya da ya cika. Sule ya cigaba da cewa ko kwamishanoni dake karkashinsa babu abun da ya dada masu. Wata irin siyasa ta kabilanci ya keyi da ta dagani sai iyalina.

Dangane da tsayar da 'yan takara a zaben kananan hukumomi da gwamnan Yobe ya ce zai yi duk da furucin shugaban INEC Farfasa Jega cewa ba ba'a yi zabe a jihohin dake karkashin dokar ta baci ba. Kana shirya zabe baya hannun Dr Yarima Ngama. Gaskiyar ita ce bai kamata gwamnan ya dage sai ya shirya zabe ba alhali kuwa jiharsa na cikin dokar ta baci.Ya ce gwamnatin Ibrahim Geidam ta shirya zata yi zabe domin masu shirya zaben na jiha ne sai abun da gwamnan yake so za'a rubuta.

Da ya koma kan abubuwan dake faruwa yanzu tsakanin APC da PDP ya ce idan Allah ya kaimu shekara mai zuwa aka kada gangar siyasa za'a sha mamaki. Mutane da yawa zasu fice daga APC su koma PDP.

Game da cewa PDP na tsoron idan Geidam yana kan mulki ba zasu ci zabe ba shi yasa suna son wa'adinshi ya kare su samu su ci zabe sai Sule ya ce ai bangaren Ibrahim Geidam ke jin tsoro dalili ke nan da suke kiran shugaba Jonathan ya cire Dr Yerima Ngama wanda yanzu ya tayar masu da hankali domin ayyukan da yake yiwa jiharsa.

Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG