Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaban Amurka Ya Kada Kuri'ar Raba Gardama


Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Mike Pence yayinda ya je majalisar dattawa domin kada kuri'ar raba gardama wurin tabbatar da ministar ilimi

Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, ya rantsar da sabuwar ministar ilimi Betsy Devos, bayan da ya kada kuri'ar raba gardama kan tantanceta wanda ya janyo kalubale ga zabenta. Wannan shine karon farko a tarihin Amurka, da za'a bukaci mataimakin shugaban kasa ya kada kuri'a domin a amince da wadda aka zaba minista.

Tun farko a wunin jiyan, senatoci 'yan Republican biyu suka hade da 'yan Democrat baki daya wajen kin amincewa da zaben Devos. Sai aka sami senatoci 50-50 a ko wani bangare, wanda yasa tilas mataimakin shugaban kasa ya kada kuri'ar raba gardama. Ita dai Devos zakara ce ga masu bin manufofin barin iyayen yara suyi amfani da kudin gwamnati wajen tura 'yayansu makarantu masu zaman kansu.

Amma Senata Lamar Alexander mai wakiltar jahar Tennesse, wanda ya rike mukamin ministan ilimi a zamanin mulkin George Bush babba, yace nada Devos ministar ilimi ya dace sosai, saboda tsarin da take goyon baya, na baiwa iyayen zabin makarantun da zasu tura 'yayansu, hakan a ganinsa, zai janyo gasa tsakanin makarantu, matakin da ya ce zai taimakawa yara marasa galihu,damar karawa da yara daga gidajen masu hali.

XS
SM
MD
LG