Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris Ta Isa Ghana


Kamala Harris a Accra
Kamala Harris a Accra

A ziyararta ta mako guda zuwa nahiyar Afrika, mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta isa kasar Ghana ranar Lahadi don tattaunawa kan batutuwa da yawa, ciki har da tattalin ariki.

Dalibai 'yan makaranta sun tarbi mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da raye-raye da kade-kade a yayin da ta isa Ghana ranar Lahadi don fara ziyarar mako guda a Afirka da nufin karfafa dangantakar Amurka, a daidai lokacin da kasashen duniya ke gogayya game da makomar nahiyar.

Yaran sun yi ta murna tare da daga tutocin Ghana da Amurka a lokacin da Harris ta sauka daga jirginta bayan da ta tashi daga Amurka cikin dare.

Kamala Harris ta gaida 'yan makaranta a Ghana
Kamala Harris ta gaida 'yan makaranta a Ghana

"kasancewa ta a nan Ghana da kuma nahiyar Afirka abin alfahari ne," a cewar Harris. "ina cike da farin ciki game da makomar Afirka."

Ta ce tana so ta karfafa batun habbakar tattalin arziki da samar da abinci, kuma zata yi amfani da damar ziyarar don "ta ga sabbin kere-keren da ake yi a nahiyar."

Ghana dai na daya daga cikin kasashen nahiyar Afrika masu bin tafarkin dimokradiyya da ke zaman lafiya, amma Harris ta kai ziyarar ne a daidai lokacin da kasar ta yammacin Afirka ke fuskantar kalubale sosai.

Harris a Ghana
Harris a Ghana

Tattalin arzikin Ghana, wanda ke daga cikin kasashen duniya da ke habbaka cikin sauri kafin zuwan annobar COVID-19, na fuskantar matsalar bashi da hauhawar farashin kayayyaki da ke haifar da tsadar kayan abinci da sauran kayan masarufi.

XS
SM
MD
LG