Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakan Da Najeriya Ta Dauka Kan Coronavirus


Shugaba Buhari na Najeriya
Shugaba Buhari na Najeriya

Yayin da kasashen duniya ke daukar muhimman matakai domin takaita yaduwar cutar Coronavirus, Najeriya ma ta bi sahu, inda ta garkame wa ‘yan kasashe 13 kofofinta.

Majalisar ministoci ta kasar karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ce ta fito da sanarwar wannan matakin.

Kakakin fadar shugaban Najeriya, Alhaji Garba Shehu ya bayyana wa wakilinmu Umar Faruk Musa cewa abu biyu ne ke fuskantar barazana a Najeriya daga wannan cutar.

“Na daya shi ne lafiyar al’umma a Najeriya, na biyu kuma shi ne tattalin arzikinmu."

“A cikin shawarwarin da gwamnati ta yi nazarinsu, mun yi duba da yadda dama farashin mai ya karye a kasuwannin duniya, sai aka ga dole a karye farashin mai a nan gida Najeriya, inda aka mayar da shi daga 145 zuwa 125 kowane lita daya,” a cewarsa.

Banda wadannan akwai matakai daban daban da gwamnatin ta dauka, kamar hana jami’an gwamnati fita daga najeriya.

'Yan Najeriya kuma masu zaman kansa an tilasta wa kowa yin kwakkwaran tunani kafin yanke shawarar yin wata tafiya.

Ga kuma ‘yan Najeriya da zasu dawo gida, sai an kebe kowa na mako biyu domin duba lafiyarsu, a tabbatar cewa basu dauke da cutar.

A cikin kasashen da Najeriya ta haramta wa zuwa kasarta, akwai Amurka da Birtaniya da China da Japan da Netherlands da Italy da Iran, da dai sauransu.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG