Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakin Gaggawa da Kasashen Duniya Suka Dauka Ya Dakile Karancin Abinci - Gutteres


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce matakin gaggawan da kasashen duniya suka dauka, ya taimaka kwarai wajen kaucewa mummunar matsalar karancin abinci a wasu kasashe na duniya, amma ya ce duk haka, har yanzu adadin mutanen da ke bukatar abinci na ci gaba da karuwa.

A watan Fabrairu, Guterres ya yi gargadin cewa mutane miliyan 20 na fuskantar barazanar yunwa a kasashen Sudan ta Kudu, da Somaliya da arewa maso gabashin Najeriya da kuma Yemen, inda ya yi kiran neman taimakon karinDala biliyan 5.6 a shekarar nan.

Sai dai ya ce, duk da cewa kasashen duniya sun kawo daukin gaggawa, har kuma aka samu kusan kashi 70 na kudaden da aka bukata, matsalar samun hanyar kai dauki ga yankunan da ke bukatar agajin, ta kawo cikas wajen raba kayayyakin abincin.

Guterres ya kara da cewa rikice-rikice da ake samu a yankunan, su suke haifar da matsalar karancin abincin.

Ya kuma ce muddin ba a kawo karshen rikice-rikicen ba,za a cigaba da fuskantar matsalar ta karancin abinci.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG