Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakin Shugaban Amurka Ya Shafi Kasashen Nahiyar Afirka


shugabannin kasashen Afirka.
shugabannin kasashen Afirka.

Shugabar kungiyar tarayyar Afrika mai barin-gado, ta nuna damuwarta kan haramtawa wasu kasashen Afrika uku da gwamnatin Amurkawa ta yin a shiga kasar.

Yayin bude taron kolin kungiyar da ake yi na shekara-shekara, Nkosazana Dlamini Zuma ta ce wannan mataki da Amurkan ta dauka ya shafi daukacin nahiyar ta Afrika.

Matakin haramta shigar Amurkan dai ya shafi kasashen Libya da Somalia da kuma Sudan, wadanda mafi rinjayen al’umominsu Musulmi ne.

Madam Dlamini Zuman, ta kara da cewa wannan mataki zai kara dagula dangantakar kasashen da Amurka, domin tun a baya ma, dangantakar dake tsakaninsu ta na da rauni.

Ministan harkokin wajen Somalia, Abdisalam Omer, ya fadawa Muryar Amurka cewa har yanzu kasarsu na da kyakyawan zaton cewa dangantakarsu da Amurka za ta samu daidaito, yana mai cewa ya yi wuri a nuna damuwa kan matakin Amurka, duk da cewa abin damuwa ne.

XS
SM
MD
LG