Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan Nijar Na Samun Horo Kan Dabarun Shiga Kasuwannin Duniya


Ministan Cikin Gidan Nijar Bazoum Mohamed

Ayyukan sarrafa kayan fatun dabbobi domin hada kayayyaki, na daga cikin hanyoyin dake samarwa Jamhuriyar Nijar kudaden shiga, saboda ‘yan yawon shakatawa dake zuwa kasar ziyara, hakan ya sa hukumomi suka fara koya wa mata yadda za su kaifafa dabarunsu a wannan fanni.

A Jamhuriyar Nijar kungiyar masu sana’ar hannu da hadin guiwar abokan hulda na ketare sun shirya wani taron horo domin fadakar da matan jihohin kasar dubarun aikin fata ta yadda za a kara ingancin kayayakin da suke kerawa don ganin sun kara samin karbuwa a kasuwannin ketare.

An fara horar da rukunin farko na matan Nijar masu ayyukan hannu kan yadda za su koyi dabarun sarrafa fata wajen hada kayayyaki irinsu jakankuna da talakma.

Matan sun fito daga wasu jihohin Nijar hudu a tashin farko inda hukumomi suka bayyana cewa shirin wani yunkuri ne na karawa mata azama wajen fadi tashin da su ke yi wajen ganin sun dogaro da kansu.

“Matan da muka debo daga jihohi su ke, yanzu cikin kowace jiha an dauko mutum bi-biyu, sannan nan gaba ma za mu dauko mutum bi-biyu a sauran jihohin.” In ji shugaban kungiyar masu aikin hannu, Ibrahim Mousa.

Shirin horar da matan in ji shugabannin kasar wani yunkuri ne har ila yau na bai wa mata damar lakantar aiki da teloli masu aiki da wutar lantarki.

“Ana samun matsala, sai mutum ya baka aiki, mai dinki daban ma’aikaci daban, ana samun matsala.” A cewar mai horar da matan, Ibrahim Mai Kasuwa.

“Sana’a babu tabewa a cikinta kowacce iri ce, kiran da zan yi shi ne kamar idan an ba da horon a rika bi ana ganin yadda harkokin ke tafiya, tunda im ba kulawa babu ci gaba. In ji Malam Hauwa’u Mai Barma, wacce ta fito daga jihar Zinder daga cikin matan da ke samun horo.

Domin jin cikakken rahoton saurari wakilinmu Sule Mumuni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG