Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan Nijar Sun Bukaci Mahukuntar Kasar Su Ceto Matan da Boko Haram Ke Garkuwa da Su


MATA MASU FAFUTIKAR GANIN AN SAKO WADANDA BOKO HARAM KE GARKUWA DA SU A NIJAR

Hadakar kungiyoyin matan Nijar ta bukaci mahukumtan kasar su gaggauta ceto mata 33 da Boko Haram ke garkuwa da su da wasu shida da suka bace wajen makonni shida da suka gabata

A karon farko tun lokacin da kungiyar Boko Haram ta soma kai hari a yankin Diffa cikin Jamhuriyar Nijar a shekarar 2015, ta sace mata 33 makonni shida da suka gabata kuma har yanzu tana cigaba da yin garkuwa da su.

Bisa ga alamu kungiyar ta fara canza salon yaki da dakarun kasar lamarin da ya sa mutane musamman mata shiga cikin wani halin zullumi.

Dalili ke nan da hadakar kungiyoyin mata suka yi taron nuna juyayinsu da takaicinsu tare da kiran mahukumtan kasar su gagauta ceto matan da aka sace a lokacin da hadakar dakarun kasashen tafkin Chadi ke ikirarin karya lagon 'yan ta'addan.

MATA MASU FAFUTIKAR GANIN AN SAKO WADANDA BOKO HARAM KE GARKUWA DASU
MATA MASU FAFUTIKAR GANIN AN SAKO WADANDA BOKO HARAM KE GARKUWA DASU

Shugabar hadakar kungiyoyin matan Madam Aliyu Cimago tana mai cewa "yau muna bakin ciki, muna kuka da hawaye da abun da ya faru cikin garin Ngalewa. A wurin aka samu yara tara aka yankasu kamar raguna. An kama mata 33 da 'yan mata guda shida an tafi da su. Har yau ba amo ba labari. Bayan sati shida da wannan abu ya faru har wa yau ba mu ji labarin komi ba saboda haka muna so mu san ina suke".

Ta cigaba da cewa yaushe za'a cetosu, su da aka rabasu da iyalansu, aka fitar dasu aka tafi dasu. Wasu matan an rabasu da mazajensu da 'ya'yansu. Tace wasu ma an kashe mazajensu kana wasu kuma ba'a san halin da suke ciki ba.

Dangane da maganar sace mutanen Ngalewa Shugaban kasar Nijar a jawabinsa na ranar biyu ga watan Agusta ya bukaci askarawan Nijar su gaggauta ceto matan da yaran su kuma mayar dasu gidajensu.

Kasancewa makonni biyu bayan jawabin shugaban kasar babu wani sabon labari ya sa hadakar kungiyoyin matan kasar kiran gwamnati ta kara jan damarar ceto mutanen.

Suna cewa a matsayinsu na mata suna goyon bayan matan Diffa saboda tunda Boko Haram ta sace masu mutane basu da kwanciyar hankali. Akwai wasu matan ma da ake daurawa bam su shiga cikin jama'a su kashe 'yanuwansu ba tare da son ransu ba.

Matan sun kira gwamnati ta san hanyar da zata bi ta ceto mutanen da ake garkuwa dasu.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG