Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matar Farko Da Ta Kamu Da Zazzabin Lassa A Jihar Ogun Ta Mutu Wata Sabuwa Ta Kamu


Beraye ne ke kawo cutar zazzabin lassa

A wani taron manema labarai Kwamishinan Kiwon Lafiya na jihar Ogun, Dr. Babatunde Efayena, ya sanar da cewa matar nan ta farko da ta kamu da zazzabin Lassa a jihar Ogun ta rasu, haka kuma wata ta biyu ta kamu.

Dr. Babatunde Efayena, yace kamar yadda ya faru ga matar farko wadda ta mutu a sanadiyar kamawa da zazzabin Lassa, itama wannan mata tayi tafiya ne zuwa jihar su ta Kogi, domin bikin aure bayan dawowarta ne ta kama zazzabi wanda ya nuna ta kamu da zazzabin Lassa, amma tana cikin hayyacinta tare da bata kulawa.

Haka kuma an gano cewa matar ta biyu tayi mu’amula da mutanen kimanin sittin, wanda yasa yanzu haka ake sanya idanu akan su. Ita dai matar farko da ta rasu za a yi mata jana’iza kamar yadda hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta tanadar.

Kwamishinan ya bukaci mutane da suyi gaggawar sanar da jami’an kiwon lafiya zarar sun shaida wani mutum yana yin zazzabi mai zafi, kuma su kori duk berayen dake muhallansu.

Domin Karin Bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:35 0:00

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG