Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa 350 Zasu Amfana Da Horaswar Aikin Gona Kyauta.


Gona

Matasa 350 daga jihohi 10 na Najeriya zasu amfana da shirin horaswar aikin gona kyauta domin yaki da rashin aikin yi.

A kokarinta na samarwa matasa da aikin yi, gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara horas da matasa aikin gona kyauta.

Matasa 350 ne da suka kammala karatun manyan makarantu daga jihohi goma zasu fara amfana da wannan sabon tsarin.

An fara wannan horaswar ce a babbar kwalejin ayyukan gona ta gwamnatin tarayya dake garin Akure a cikin jihar Ondo.

Da yake bude bikin horaswar a cikin babban kwalejin aikin gona, shugaban kwalejin Dr Samson Odedina yace ana ba da wannan Horon ne a bisa umurnin Ministan Ayyukan gona da raya karkara Chief Abdu Ogbeh.

Yace ana sa ran baiwa matasan wannan horon ne domin su zamo masu dogaro da kansu, wanda za a basu jarin da zasu fara amfani da shi a matsayin share fage.

Ga Hassan Umaru Tambuwal da bayani 2’30

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG