Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A cigaba da yakar 'yan Boko Haram, a Jamhuriyar Nijar, kungiyoyin Fararen Hula sun dauki wuka da nama domin bankado mayaka da makaman Boko Haram.

Wakilin Muryar Amurka Chiabou Mani ya samu jin ta bakin Malam Abdu Dan Naito na kungiyar Farar Hula Codae Reshen Jihar Maradi. Malam Abdu, yace Wanna abu dake faruwa, abune na tir da Allah wadai.

Malam Abdu Dan Naito, ya kalubalanci hukumomi inda yace inna jami'an tsaron da 'yan sandan ciki suke har 'yan kungiyar Boko Haram suka samu nasarar tara irin wadannan makamai, a cikin garin Diffa, yana mai cewa wannan na nuni da cewa akwai tabarbarewar tsaro.

Ya kara da cewa tsaron kasa ya kunshi kowa da kowa dake zaune cikin kasa, ya kuma yi kira ga jama'a, dasu sanarda hukumomi duk wani abu da basu gane ba.Ya kuma gargadi matasa da kada su kuskura su yarda kwadayi ya jasu domin kwadayi ma budin wahala ne.

Matasa Kwadayi Mabudin Wahala - 3'03"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

XS
SM
MD
LG