Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Zasu Yi Maci Zuwa Majalisar Dokokin Najeriya Talatan Nan, Domin Neman A Yi Gyara Ga Tsarin Mulki


Daliban wata jami'a a Najeriya suke zanga zanga

Matasan suna son a rage shekarun da mutum zai kai kamin ya sami ikon tsayawa takarar zabe.

Matasa zasu yi gangami a safiyar yau Talata zuwa harabar majalisar dokokin kasar a Abuja, domin matsa lamba na ganin wakilan sun yi kwaskarima ga dokokin da suka kayyade shekarun yin takara.

Matasan sun fusata ne domin wakilan sun jingine batun yin kwaskwarima ga sashen tsarin mulki da ya kayyade shekarun da dan mutum zai kai kamin ya tsaya takara.

Hamza Lawal wand a yayi magana a madadin matasa, yaje zanga-zangar su ta lumana ce kuma zasu yi bakin kokarinsu na ganin majalisa ta saurare su.

Da aka tambaye shi, me zasu yi idan hakar su bata cimma ruwa ba, Hamza ya yi barazanar cewa, matasa sune rabi ko ma fin haka na masu zabe a Najeriya. Yace duk wakilin da yayi biris da bukatun su zai hadu da fushin su a zaben shekara ta 2019.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:50 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG