Accessibility links

Wasu Gwamnonin Arewacin Najeriya sun kaiwa Gwamna Rotimi Ameachi na jihar Ribas ziyara domin jin-jina masa, yayinda jiharsa ke fama da rikicin siyasa. Sai dai an yi musu maraba da iyu da jifa.

Wakilin Muryar Amurka Lamido Abubakar ya bada labarin cewa Gwamnonin sun hada da na jihar Adamawa Murtala Nyako, da Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, da na Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso da ma na jihar Neja, Babangida Aliyu.

Saukarsu ke da wuya a tashar jirgin sama na wannan jiha, Gwamnan Ribas Rotimi Ameachi ya tarbe su.

Sai dai wasu mutane basu ji dadin wannan ziyara ta Gwamnonin Arewan ba, inda suka rika daukan duwatsu suna jifansu, suna yi musu ihu, wasu kuma na dauke da kwalaye masu dauke da sakonni dake cewa basu son Gwamnan jihar Ribas, Rotimi Ameachi.

Kawo yanzu ba’asan daga inda matasan suke ba. Su kuma Gwamnonin basu bayanna ko mene ya kaisu jihar Ribas ba.

XS
SM
MD
LG