Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Kai Gwamnatin Zamfara Kotu


Gwamna Abdul'aziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya.

Rashen jihar Zamfara na majalisar ta matasan arewane dai suka gurfanar da gwamna da gwamnatin jihar harma da majalisar dokokin jihar agaban babbar kotun tarayya dake garin gusau.

Inda take kalubalantar kudurin gwamnati na sayar da hannayen jari mallakar gwamnatin jihar, dakuma kanananan hukumominta wadanda ke kamfanin samar da wutar lantarki na Nija Delta da kudinsu ya kama naira miliyan dubu ashirin da hudu.

Shugaban rashen jihar Zamfara na majalisar ta matasan Arewa Marir Haidara Kaura, yana ganin matakin na da illa ga makomar matasa a wannan jihar, yace “wanan abu bai dace kuma zai cutar ma ilahirin al’ummar jihar Zamfara shiyasa mukaga ya dace Mukai wannan kara.”

Saurari wakilinmu Murtala Faruk kuji cikekken rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG