Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Suna Da Damar Bada Gudummuwa A Kasa: J.T. Useni


Saneta Jeremiah Hussaini
Saneta Jeremiah Hussaini

Dan takarar gwamnan jihar Plato karkashin tutar jam’iyar PDP Saneta Jeremiah Useni ya bayyana cewa, duk da yake burin matasa da dama na tsayawa takara a zaben shekara ta dubu biyu da goma sha tara bai cika ba, suna da rawar da zasu taka a harkokin mulki.

Saneta Useni wanda ya rike mukamai da dama karkashin mulkin soja da ya hada da ministan babban birnin tarayya Abuja, yace dokar da majalisa ta kafa da shugaban kasa ya sawa hannu domin ba matasa damar tsayawa takara da ake kira “Not Too Young To Run” an kafa ta ne da nufin ba matasa lokaci su kara nazarin harkokin mulki kafin shiga siyasa gadan gadan, sabili da haka aka bada tsawon shekaru kafin ta fara aiki.

Janar Useni wanda ya kasance dan takakarar gwamna mafi yawan shekaru a zaben na bana, yace, yana jin yafi wadansu masu jini a jika kuzari, sabili da haka baya ganin shekarunsa a matsayin wata kalubala. Dangane kuma da delilin da yasa bai nemi tsayawa takarar shugaban kasa, ba ganin shekarunsa da kuma mukamai da ya rike a baya, Janar din da aka fi sani da J.T. Useni yace, lokacin da al’ummarsa suka neme shi ya tsaya takara, sun bukace shi ne ya tsaya takarar gwamna, abinde kuma ya yi ke nan.

Daga cikin matsalolin da yace zai maida hankali a kai idan aka zabe shi gwamna akwai batun shawo kan matsalar harkokin tsaro da samar da ayyukan yi tsakanin matasa da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.

Yace jihar Plato ta yi fama da tashe tashen hankali da rikicin addini da kabianci da suka gurguntar da harkokin noma, da kasuwanci da tattalin arzikin jihar, sabili da haka akwai bukatar samun wanda yake da karfin hali da kwarewa da kuma hangen nesa, kuma bisa ga cewar shi, ya mallaki wadannan duka.

Saurari cikakkar hirar su da Alheri Grace Abdu

Hira da J.T.Useni-3:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG