Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Arewacin Najeriya Na Neman Mafita Kan Rikicin Kudancin Kaduna


KADUNA: Rikicin Kafanchan
KADUNA: Rikicin Kafanchan

Hadakar Kungiyoyin matasan arewacin Najeriya sun shirya tarurruka da nufin nemo mafita ta dindindin game da wannan rikicin da ake fama da shi a Kudancin Kaduna da ya yi sanadin rasa rayuka da kaddarori.

Taron hadakar kungiyoyin Arewacin Najeriyan da ya zakulo wakilai daga kananan hukumomin kudancin Kaduna baki daya ya cimma matsayar kafa wasu kwamitoci da za su lalubo mafita game da matsalolin da aka gano.

A cikin hirarsa da Sashen Hausa, Alhaji Nastura Ashir Sheriff, shugaban kwamitin amintattu na hadakar kungiyoyin Arewacin Najeriya ya bayyana cewa, an kafa kwamitoci guda uku bisa ga abinda aka gano a wannan zaman da ya hada da kwamitin da zai kula da zamatakewar al'ummar, da siyasa, da kuma na tattalin arziki, wanda zai duba matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa da shaye shaye da ake gani sun taimaka wajen ruruta rikicin.

An kuma kafa kwamitin da zai duba abinda ya shafi gwamnati, wanda zai maida hankali wajen neman abinda ya kamata gwamnati ta yi domin ganin an shawo kan wannan matsalar.

Shugabannin kwamitocin da aka kaddamar sun hada da Paul Wani da ke shugabantar kwamitin inganta rayuwar al'umma, da Reverend Bitrus Dangiwa shugaban kwamitin kula da harkokin mulki, da kuma Alhaji Bala Adamu shugaban kwamitin harkokin siyasa, tattalin arziki da kuma zamantakewar al'umma.

Shugabannin kwamitocin sun bayyana cewa zasu shiga karkara su tattauna da al'umma domin neman hanyar samun masalaha. Bayan kwamitocin sun yi tuntuba sun kuma harhada rahotanninsu, zasu koma babban zauren domin daukar matakan aiwatarwa.

Banbancin addini da kabilanci na cikin matsalolin da hadakar kungiyoyin Arewacin Najeriyan ta gano suna rura wutar rikicin kudancin na Kaduna da suka bayyana cewa ana amfani da matasa wajen cimma burin.

Duk da Hare-haren 'yan-bindiga a yankin kudancin Kaduna ya yi sauki a 'yan kwanakin nan, kungiyoyi daban-daban na ta yunkurin ganin an yiwa tukka hanci don kawo karshen matsalar tsaro a yankin kudancin Kaduna baki daya.

Saurari rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti:

Matasan Arewacin Najeriya Na Neman Mafita Kan Rikicin Kudancin Kaduna:3:53"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG