Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasan Nijar Sunyi Gargadi Kan Tafiya Aikin Ci Rani A Ketare.


'Yan ci rani masu neman tafiya turai daga Libya.

Matasan sun komo daga Libya, yanzu sun kama aikin noma.

Wasu matasa daga jamhuriyar Nijar wadanda suka tafi cin-rani a kasar Libya, sun komo gida, kuma tuni suka rungumi noma.

Muhammadu Seni, wanda yana daga cikin wadannan matasan, yana kira ga sauran sa’o’insa wadanda suke tunanin barin kasashensu da zummar aikin ci rani a kasar Libya, da su sake tunani. Seni yace a saboda tabarbarewar harkokin tsaro a Libya, suna samun na ci da sha, amma cikin fargaba.

Amma yanzu lamarin ya kai ga cewa, abunda ya kai su kasar na neman kudin jari da zai basu damar sayen kayan aikin gona, hakan sam bashi yi yuwa.

Wannan mataki da suka dauka yasa shugabannin a wasu yankin Nijar din tallafawa matasan ta wajen sama musu kayayyakin aiki.

Magajin garin Chintabaradun Ahemd Dan-Musa, ya yaba da tunanin matasan, shi yasa ma hukuma taga bukatar ta dafa musu, kamar yadda ya gayawa wakilin Sashen Hausa Haruna Mammane Bako.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG