Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Thailand Da Aka Ceto A Karon Farko Sun Bayyana a Bainar Jama'a.


Mako guda bayan da aka ceto su daga wani kogo da suka makalle a cikinsa, yanzu haka matasan ‘yan kwallon kafar nan na kasar Thailand da kocin su na kan hanyarsu na komawa gidajensu don sake hadewa da iyalan su.

An salami tawagar 'yan kwallon kafa daga wata asibiti da ke arewacin garin Chaing Rai, inda daga nan ne za’a kai su wani waje inda zasu yi fitowar su ta farko a bainar jama’a tun da aka ceto su.

Tawagar za su amsa tambayoyin manema labarai a hirar da aka shirya za su yi da manema labaran har tsawon minti 45 wanda za a nuna a kafofin yadda labarai a kasar.

Jami’ai sun ce samarin da shekaransu na haihuwa suka kama daga 11 izuwa 16, da mai horaswar su duk na cikin koshin lafiya, amma likitoci na da damuwarcewa mai yiyuwa ne yaran kan iya fuskantar matsalar shiga rudami nan gaba idan suka tuna abin da ya same su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG