Accessibility links

Wasu 'yan Najeriya, musamman a Maiduguri, sun ce kamar su na kurkuku don ba su iya kira ko karbar kira a wayoyinsu.

Makonni da dama a bayan da kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnati Lidda'awati Wal Jihad, wadda aka fi sani da sunan Boko Haram, ta dauki alhakin kai hari a kan wasu cibiyoyin sadarwa na wayoyin salula a sassan kasar, mazauna wasu daga cikin wuraren da abin ya shafa sun ce ji suke yi kamar su na kurkuku, inda wayoyinsu ab su aiki yawancin lokuta, kuma ba su da hanyoyin shiga Intanet.

Wakiliyar Muryar Amurka Heather Murdock ta ce idan mutum yayi kokarin kiran wasu jihohin arewacin Najeriya daga Abuja, musamman wadanda ke yankin arewa maso gabas, yawancin abinda zai ji shi ne sakon cewa ko dai wayar tana kashe, ko kuma ya ji kamar ana amfani da wayar.

Wani wakilin Muryar Amurka a Maiduguri ya ambaci mazauna birnin su na kukar cewa harkokinsu na kasuwanci sun fara ja da baya, kuma sun fara fargabar cewa wannan abu zai kai su ga talaucewa ganin da ma dai ba wani karfi suke da shi ba.
Gawarwaki na wadanda ake zaton 'yan Boko haram ne a kusa da wata motar 'yan sanda a Maiduguri, ranar 31 ga watan Yulin 2009, lokacin mummunan gumurzun da aka yi a tsakanin jami'an tsaro da 'ya'yan kungiyar.
Gawarwaki na wadanda ake zaton 'yan Boko haram ne a kusa da wata motar 'yan sanda a Maiduguri, ranar 31 ga watan Yulin 2009, lokacin mummunan gumurzun da aka yi a tsakanin jami'an tsaro da 'ya'yan kungiyar.


Maiduguri dai ita ce cibiyar kungiyar Boko Haram, wadda a kwanakin baya ta yi ikirarin cewa ta kai hare-hare kan turakan kamfanonin salula a garuruwa da dama a saboda tana zarginsu da laifin taimakawa gwamnati wajen bin sawun 'ya'yanta da ake kamawa.

Kamfanonin sadarwa na wayar salula a Maiduguri, sun yi alkwarin gyara turakan, amma sun roki jama'a da su kara nuna hakuri. Sai dai kuma wani ma'aikacin kamfanin salula da ya nemi kada a bayyana sunansa, yace ma'aikatan da ya kamata su yi wannan gyara sun ki yi saboda fargabar cewa za a kai musu farmaki lokacin da suke aikin.

Da yawa daga cikin ma'aikatan ma sun gudu sun bar Maiduguri.

Jami'an tsaro sun yi alkawarin kara yawan 'yan sandan da zasu yi gadin cibiyoyin sadarwa. Amma a Najeriya, su kansu sojoji da 'yan sandan kasar, kamar kowa ma, sun dogara ne a kan wayoyinsu na salula domin sadarwa, tunda layukan tarho na kasa sun lalace.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG