Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Sha da Safarar Miyagun Kwayoyi Na Kara Habaka a Najeriya


Yakubu Kibo kwamandan NDLEA na Jihar Adamawa shi ne ta hannun dama hodar ibilis da aka boye cikiin wata naura

A wani shigan burtu da wakilin Muryar Amurka dake Adamawa ya yi, ya gano cewa matasa da matan aure suna dada shiga shan miyagun kwayoyi tare da safararsu

Rahotanni na cewa yanzu haka a Najeriya, matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi sai kara habaka ta keyi, musamman a arewacin kasar kuma a wurin matasa, yayin da a bangare guda kuma jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyin ta NDLEA, take fuskanci turjiya daga masu ta’ammali da kwayoyin, lamarin da kan jawo fito-na-fito a wasu lokuta.

Hodar ibilis cikin naurar da aka boyeta da NDLEA ta kama a jihar Adamawa
Hodar ibilis cikin naurar da aka boyeta da NDLEA ta kama a jihar Adamawa

Wannan batu yanzu haka na kara tada hankulan iyaye ganin cewa har da mata a harkar sha da fataucin kwayar.

Alal misali a jihohin Adamawa da Taraba, har kungiyoyi irin wadannan matasa ke kafawa, kuma masu ta’ammali da kwayan sun hada har da mata, kamar yadda wakilin Muryar Amurka, Ibrahim Abdulaziz ya tarar a wata matattarar yan jagaliya da da yiwa shigan burtu.

Shima Mr Yakubu Kibo dake zama kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar Adamawa ya tabbatar da cewa mata sun tsundumma dumu-dumu cikin wannan dabi’ar ta shaye-shaye.

To sai dai kuma ganin yadda wannan matsala ke kara ta’azzara ne yasa wasu kungiyoyi yunkurowa domin fadakar da al’umma game da illar dake akwaia cikinta.Mr Shehu Yohanna, wanda jigo ne a majalisar matasan Najeriya ta NYCN, ya ce abun takaici ne abubuwan dake faruwa.

Manazarta na ganin dole a hada hannu domin yakar wannan matsala ta shan kwaya da matasa ke yi. Shekarau Yerima, wani dan jarida a Yola, ya ce su ma kafafen yada labarai dole su tashi tsaye.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG