Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Tsaro A Jihar Zamfara


Gwamna Abdul'aziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara,

Can baya jihar Zamfara ta yi fama da yawan kai hare hare, kashe kashe, kona gidaje, satar mutane da dabbobi da suka dan lafa, amma yanzu sha'anin rashin tsaro a jihar na neman sake zama ruwan dare gama gari.

Sha'anin rashin tsaroa a jihar na kokarin canza sabon tarko saboda yanzu 'yan bindiga sun tsunduma wajen satar mutane walau a hanya ko a gidajensu tare da neman kudin fansa.

Malam Dawa wani dan sa kai a yankin karamar hukumar Maru ya ce 'yan bindigan ke dauke mutane a gidajensu ko su taresu akan hanya su kaisu daji su kashe. A cewar Malam Dawa akwai lokacin da suka dauki mutane 11 suka kashe takwas cikinsu.

Inji Malam Dawa da zara 'yan bindigan sun dauki mutane sai su kaisu su ajiye kana su dawo a basu kudi. Wani ya biya Nera miliyan biyu' ko uku ko hudu. Mara karfi kuma har dubu dari suna amsa. Idan kuma ba'a ba da kudi ba sai su kashe.A cewarsa babu abun da jami'an tsaro zasu yi ko suke kokarin yi duk da korafinsu da suka mika wa mahukumtan.

Sai dai a wata fira da gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya yi da Muryar Amurka kwanakin baya ya zargi 'yan sa kai da wasu al'ummar jihar da kara ruruta wutar hare haren.

A cewar gwamnan, gwamnati ta na daukan duk matakin da yakamata ta dauka amma matsalar ta na da nasaba ne da wasu bata gari da suke kara haddasata. Akwai wasu bata gari da suke ganin zasu iya kare mutanensu alhali kuwa basa iya karesu, inji gwamnan. Ya ce yawancin kisan da ake yi na ramuwar gayya ne.

Aminu Bala Sokoto wani tsohon soja na mayakan sama, mai sharhi akan lamuran tsaro na ganin wajibi ne gwamnatocin Zamfara, Sokoto, Kebbi da Katsina su hada karfi da karfe su tunkari abun dake faruwa muddin ana son kawo karshen matsalar.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG