Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalolin Dake Maida Hannun Agogo Baya a Aiyukan Ci Gaban Kasashen Duniya


Kungiyar tarayyar Turai ta ware Euro Miliyan 50, domin tallafawa kasar Nijar ta fuskanci wadannan matsaloli

Matsallar tsaro da ta bakin haure da matsalar canjin yanayi na kan gaba akan matsalolin dake maida hannun agogo baya a aiyukan ci gaban kasashen duniya masamman kasashen masu tasowa.

Dalili Kenan da kungiyar tarayyar Turai ta ware Euro Miliyan 50, domin tallafawa kasar Nijar ta fuskanci wadannan matsaloli.

Kwamishina kungiyar tarayyar Turai, mai kula da huldan kasa da kasa da ci gaba Mr.Mimica Neven, ya ce “Jami’an mu shirye suke su hada gwiwar da Nijar, domin tafiyar aiyukan wannan shirin saboda haka muna jiran shawarwari na zahiri dag bangasren ku dagane da bukatun wannan kasa a fannonin da shirin ya kunsa ta yarda zamu gaggauta fitar da wadanan kudade a fara aiki akan lokacin da aka tsayar kamar yada mataimakiyata ta alkawarta a ziyarar da ta kawo a watan Satumban da ya gabata.”

Kungiyar ta EU ta kara kebe wasu kudadan na daban domin fanin walwalar aluma,kamar yadda Kwamishina kungiyar EU, mai kula da huldan kasa da kasa da ci gaba ya ce “Jama’a maza da mata dake warin wannan biki ina mai farin cikin sanya hannu akan wannan yarjejeniya da ta kunshi miliyan 36, na Euro domin karfafa aiyukan kiwon lafiya ga al’umar Nijar, masamman mata da yara kanana da aiyukan bada ilimi ga ‘yan mata.”

Ministan harkokin wajen jamhuruyar Nijar, Madam Aisha Kane Bulama, ta bayana cewa tuni kasar ta shirya wata tawagar manyan jami’an, da zasu halarci taron da kasashen duniya ke shirin gudanarwa a birnin La Valek kan batun bakin haure.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

XS
SM
MD
LG