Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan Najeriya tare da sauran Jami'an Tsaro Zasu Murkushe Boko Haram


Mr. Solomon Arase babban sifeton 'yansandan Najeriya
Mr. Solomon Arase babban sifeton 'yansandan Najeriya

Mataimakin babban sifeton 'yansandan Najeriya mai kula da shiya ta 12 da ta hada da jihohin arewa maso gabas Mr. Tunde Ogunshakin yace zasu murkushe kungiyar Boko Haram tare da hadin kan sauran jami.an tsaro cikin wa'adin da shugaban kasa ya diba masu.

Mr. Ogunshakin yace sun sha alwashin murkushe 'yan ta'ada ko ta halin yaya cikin wa'adin da shugaban kasa ya basu.

Shi ma sarkin Bauchi ya yabawa shugaban zaman lafiya da yanzu ana samu musamman a jihar Bauchi. Kazalika sabon kwamishanan 'yansandan jihar yace sai ya kimtsa kana zai san irin matakan da zasu dauki domin cigaba da samun zaman lafiya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG