Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matukar Ban Sami Nasara A Zabe ba Zan Mika Ragama – Inji Shugaba Jonathan


Shugaba Jonathan tare da 'yan jarida suna tattaunawa.
Shugaba Jonathan tare da 'yan jarida suna tattaunawa.

A zantawar Shugaba Jonathan da manema labaru wanda yafi maida hankali kan tsaro, da ya zama hujjar ‘dage zabe a Najeriya.

Shugaba Jonathan dai yace, “Tun zaben 2011 nace zan gwada missali a Afirka, na matukar ban sami nasara a zabe ba zan mika ragama ga wanda yayi nasara.” Jonathan dai ya bada tabbashin za’a gudanar da zabe da rantsar da duk wanda yayi nasara ranar ashirin da tara ga watan Mayu.

Aliyu Sarkin Fada na daga masu kada kuri’a daya kalli zantawar ta Shugaba Jonathan, Aliyu yace, “maganganun dayayi akwai wadansu wuraren dana kama naga cewar magana ce wadda yace in har bai sami nasara ba, zai sauka ya bayar da mulki,” yaci gaba da cewa, kuma yace yana son a shiga cikin tarihi a kasashen Afirka, na shugaba na farko da ya sauka ya bayar da mulki, kuma wanna na nunin cewa shi shugaban na shakku kan zaben da za’a yi.

Mutane dayawa dai na fatan cewa alwashin zai zamo gaskiya, kuma Allah yasa ayi cikin kwanciyar hankali.

Mataimakin daraktan kamfe na shugaba Jonathan, Isa Tafida Mafindi yace zantawar zata kwantar da rade radin dake nuna gwamnati ba zata bari ayi zaben ba, inda yace, “Mutane dayawa suna ta yada jita jita cewa zaben nan bazai yiwu ba, za’ayi gwamnatin rikon kwarya,” yaci gaba da cewa shugaba Jonathan ya dauki alkawarin cewa zaben zai yiwu.

Kodai da yake shugaba jonathan yace zai kwada missali a matsayin shugaba na farko da zai mika mulki matukar bayyi nasara ba Afirka, to wata kila bai tuno da tsohon shugaban Zambiya bane kenneth Kaunda, wanda ya fadi zabe a shekara ta 1991 ya mika mulki ga marigayi shugaba Frederick Chiluba.

Saurari cikakken rahotan Nasuru Adamu.

Jonathan Da Manema Labarai - 2'59"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG