Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maya Gabeira Ta Kafa Tarihi A Wasannin Kan Igiyar Ruwa


Maya Gabeira

Hukumar da ke kula da wasannin kan igiyar ruwa ta duniya wato WSL ta sanar jiya Alhamis cewa shaharariyar ‘yar wasar nan ‘yan kasar Brazil mai suna Maya Gabeira ta doke tarihin da ta kafa a duniya a wannan shekarar a lokacin da ta hau kan igiyar ruwa mai nisan mita 22.4 a tekun Nazare na kasar Portugal, daidai wurin da ta kafa tarihi a 2018.

Gabeira ta doke tarihin nata ne da kusan mita biyu a lokacin gasar da igiyar ruwan tayi sama sosai a Nazare a ranar 11 ga watan Fabrairu. Ba wai kawai wani sabon tarihi ne na mata ba, amma hukumar WSL ta ce shi ne babbar igiyar ruwa da mace ko namiji suka hau a 2020.

Wannan tarihin ya zama abin fahariyar gaske ga Gabeira wacce ta karya kafarta kuma ta kusan nitsewa a daidai wurin a 2013.

Facebook Forum

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG